Shugabannin Turai sun hallara yayinda ake ci gaba da sasantawa

Shugabar gwamnatin kasar Jamus, Angela Merkel ta shaidawa majalisar dokokin kasar cewa tilas ne yanzu a warware raunin da kasashen da ke amfani da kudin Euro ke da shi yanzu ko kuma ba za a taba yi ba.

Da take magana kafin ta wuce wajen wani babban taron kolin kungiyar tarayyar Turai, inda shugabannin suka sha alwashin warware matsalar, Mrs Merkel ta ce akwai bukatar inganta tasirin da kudin da aka ware dan tallafawa kasashen zai yi, ba tare da sun kara sa kudi a asusun dake da dala biliyan dari shida ba.

Ta ce muna bukatar duba gaba, ya kamata mu gano bakin zaran warware wannan matalar tun daga tushe.

Mrs Merkel ta ce wasu daga cikin matakan da za'a daukar za sui matukar shafar Jamus wadda ita ce tafi karfin tattalin arzuki a nahiyar Turai.

Ana dai ci gaba da zazzafar tattaunawa kan shawo matsalar basukan da yankin ke fuskanta, amma tuni masu aiko da rahotanni sun ga n o muhimman shawarwarinda za su bayar.

Wadanda suka hada da masu ba kasar Girka bashi su rage wani babban kaso na bashin da suke bi, da kuma kara kudi a asusun da suke da shi, domin tabbatar da samawa kasashen dake da karfin tattalin arzuki kamar Italiya da Spain idan suna bukatar karin bashi.