An kashe mutane biyar a Afghanistan

Image caption Taswirar Afghanistan

Wani bam da ya tashi a kusa da wata tankar mai a kasar Afghanistan ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane biyar.

Wasu mutanen fiye da arba'in kuma sun samu raunuka a fashewar wacce ta auku a arewacin kasar.

Wani jami'i a lardin Parwan da ke arewacin birnin Kabul ya ce fashewar wani abu ne ya janyo man da ke cikin motar ya soma tsiyayewa.

Ya kara da cewa a lokacin da mutane suka fara taruwa domin diban man ne sai aka samu mummunar fashewar wani abu mai karfin gaske abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutanen.