An ci zarafin Kanar Gaddafi kafin kisansa

Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Ran Shugaba Putin ya baci

Majalisar rikon kwaryar Libya ta tabbatar cewa za ta gudanar da bincike a kan rahotannin cewa an ci zarafin Kanar Gaddafi lokacin da aka kama shi gabanin a kashe shi.

Wani hotan bidiyo da aka dauka da wayar salula na abin da ya faru, wanda aka kunna tare da rage gudunsa, wanda ya kara nuna abubuwa sosai, shi ne ya kai ga sabbin zarge-zargen.

Tuni dama gwamnatin rikon kwaryar ta fara gudanar da bincike kan ko an yi masa kisan gilla ne bayan da aka kama shi makon jiya.

Firaministan kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana takaicinsa bisa hotunan bidiyon Kanar Gaddafin da aka dauka jim kada kafin mutuwarsa.

Ya ce an nuna gawarsa a gidajan talabijin na kasashen duniya, ba za ka kalla ba tare da ka ji zuciyarka ta dugunzuma ba.