Kwarin gwiwa kan taron kasashen Turai

Euro Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugabannin na fuskantar matsin lamba kan rikicin

Majalisar dokokin Jamus ta amince da bukatar da shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta gabatar, na bunkasa asusun tallafawa tattalin arzikin Turai.

Wannan zai baiwa Angela Merkel kwarin gwiwar halartar taron shugabannin Tarayyar Turai da za a yi a Brussels kan matsalar tattalin arzikin yankin.

Nan gaba a ranar Laraba ne shugabannin za su tattauna a Brussels inda suke duba yuwuwar neman taimako daga kasashen da tattalin arzikinsu ke kan ganiyar bunkasa.

Manufar ita ce a kafa wani sabon asusun saka jari da zai nemi gudunmawar kudi daga kasashe irinsu China da Brazil.

Haka nan shugabannin na kuma duba yuwuwar neman agaji daga Asusun Bada Lamuni na duniya, IMF ga gwamnatocin dake cikin matsalar.

'Yan majalisa 503 suka amince inda 89 suka nuna adawa, yayin da hudu suka kaurace domin a kara karfafa asusun.

A jawabin da ta gabatar ga 'yan Majalisun dokokin kasar, Angela Merkel ta shaida wa 'yan Majalisun cewa lallai akwai bukatar a magance raunin da ake fuskanta a kasashen dake amfani da kudin Euro.

A cewarta, kasar Jamus ba za ta ci gaba ba, matukar nahiyar turai na fama da matsaloli, inda ta ce Jamus na son ganin kasar Girka ta tsaya da kafafunta.

Ta ce Jamus ba za tayi kasa a guiwa ba wajen ganin ta bi hanyoyin da za su kyautata dangantakarta da kasar Girka.

"Al'ummomin kasar Girka sun sha fama, kuma muna jinjina musu. Suna bukatar kwarin guiwa daga sauran kasashen dake amfani da kudin Euro, akwai bukatar mu kara matsa kaimi wajen shawo kan matsalar da kasar ke ciki".

Abubuwan da ake son cimmawa

* Bankunan Turai za su kara karfin jarinsu da fiye da euro biliyan 100 domin kaucewa asarar da ka iya biyo baya, idan aka tilasta musu yafe wani bangare na bashin da suke bin kasar Girka.

* Za a kara karfin Asusun tallafawa tattalin arzikin Euro na - euro biliyan 440, sai dai babu tabbas kan hanyar da za a bi wajen yin hakan.

* Za a nemi masu bin Girka bashi su yafe mata sama da kashi 21 da aka gabatar a yanzu.

Sai dai akwai sabani tsakanin manyan kasashen da ke amfani da kudin na Euro.

Faransa ta yi fatan babban bankin Turai (ECB), zai tallafawa Asusun da bashi wanda zai karfafa Asusun da euro tiriliyon 2-3.

Sai dai Angela Markel ta nuna adawa da wannan tunanin.

Karin bayani