Duniya na fuskantar kalubalen yawan jama'a

Yawan jama'a Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jama'a na karuwa cikin sauri a sassan duniya daban-daban

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana cewa ana fuskantar babban kalubale a sakamakon karuwar yawan jama'ar duniya.

Hakan na zuwa ne gabanin fitar da wani rahoto a ranar 31 ga watan nan na Oktoba, lokacin da Majalisar za ta yi hasashen cewa yawan al'umar duniya zai kai biliyan bakwai.

Fiye da shekaru goma kenan da yawan al'umar ya haura biliyan shida, kuma adadin na karuwa da mutane dubu dari biyu a kowace rana.

Rahoton na cewa maimakon a rika kokwanto ko yawanmu ya wuce kima ne? kamata yayi a maida hankali wajen irin matakan da suka kamata a dauka wajen kyautata yanayin zamantakewa.

Rahotan ya ce akwai abubuwa da dama da za'a yi farin cikin da faruwa game da yadda batun yawan jama'a a duniya, musamman abin da ya shafi tsawon rai da dan'adam kan yi, wanda ya karu daga shekaru 48 da aka kiyasta a shekarun 1950 zuwa shekaru 68 a yanzu. A wannan lokaci ne kuma adadin yawan 'ya'yan da mata ke haihuwa ya ragu, sai dai akwai mutane da dama wadanda ke cikin shekarun da ake iya samun haihuwa, da ake sa ran adadin su zai ci gaba da karuwa.

'Kamata ya yi mu fara shiri'

Duk da cewa an samu raguwar yawan haihuwa, Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa mutanen dake doron kasa za su kai biliyan 8 nan da shekarar 2025.

Yayin da a shekarar 2050 kuma, adadin mutanen zai kai biliyan 9 kana kuma ya haura mutane biliyan goma a karshen karni.

Richard Kollodge shi ne editan da ya wallafa rahoton, ya kuma bayyana cewa, yanzu ba lokaci ne ba na tada hankali, illa dai lokaci ne da ya kamata a dauki mataki.

"Yawan mutanen da ke duniya zai ci gaba da `karuwa kuma kamata ya yi mu fara shiri, mu tabbatar cewa mutane da dama suna cikin koshin lafiya kuma sun samu ilimi.

Muna da dama yanzu a duniyar da muke ciki mai yawan mutane biliyan 7 mu samarwa kanmu kyakkyawar makoma, yayin da ake hasashen cewa yawan mutane a duniya zai kai biliyan 10, kuma lallai kamata ya yi mu dauki mataki yanzu".

Majalisar dai ta damu matuka, cewa kasashe matalauta da dama musamman kasasshen Afrika dake kudu da Sahara, karuwar yawan jama'a ka iya haifar da koma baya wajen bunkasar tattalin arziki, lamarin da ka iya jefa al'ummomi masu tasowa cikin yunwa da `kangin talauci.

Majalisar ta kara da cewa tana taimakawa mata wajen samar musu da 'yanci da hanyoyin samun kudaden shiga a matsayin daya daga cikin hanyoyin samun daidaito na karuwar al'umma tare kuma da kawar da talauci.

Kasashe da dama dai da suka hada da Jamus da Rasha da Brazil da kuma China za su samu raguwar yawan al'ummominsu cikin shekaru masu zuwa, inda kuma aka yi hasashen cewa yawan mutanen dake duniya zai fara raguwa ne bayan an shafe rabin shekaru a karni na gaba.

Karin bayani