Paul Biya ya mayar da martani ga 'yan adawar Kamaru

Image caption Paul Biya

Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya, ya mayar da martani dangane da korafe-korafen da wasu 'yan takara da suka fafata da shi a zaben da aka gudanar a kasar suka yi.

Shugaban ya yi wannan raddi ne a yayin da ya gabatar da jawabi a karo na farko bayan zaben shugaban kasa, inda aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Haka kuma ya gabatar da ire-iren manyan ayyukan da zai sa a gaba daga shekara ta 2012, da kuma yadda yake ganin makomar kasar za ta kasance.

'Yan takarar dai sun bukaci kotun kasar da kada ta amince da sakamakon zaben amma ta yi watsi da bukatar.