Ana taro kan tattalin arzikin Turai

Image caption Tutar kungiyar Tarayyar Turai

Shugabannin kasashen Turai na gudanar da taro a birnin Brussels na kasar Belgium a yau Laraba inda suka yi alkawarin cimma yarjejeniya dangane da yadda za a warware rikicin bashin da ya addabi yankin.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne akan bashin kasar Girka, da kuma yiwuwar kara yawan kudaden da ke cikin asusun ceto tattalin arzikin kasashen nahiyar.

Wannan ita ce ganawarsu ta biyu cikin kwanaki hudu.

Mataimakin sakataren baitul malin Amurka, Charles Collyn, ya ce gwamnatin Obama na da kwarin gwiwar cewa za a cimma yarjejeniya mai karfi a taron kasashen Turan.