An gabatar da matakan ceto tattalin arzikin Turai

Image caption Shugabannin Tarayyar Turai

Shugabannin kasashen Turai sun bayar da sanarwar daukar wasu matakai da za su warware rikicin tattalin arzikin da yankin ke fuskanta.

Shugaban Faransa, Nicholas Sarkozy, wanda ya gana da manema labarai bayan kammala taro a birnin Brussels, ya ce daga cikin matakan akwai tilastawa bankunan kasashen Tarayyar Turai don su yafe kashi hamsin cikin dari na bashin da suke bin Girka.

Idan suka yi hakan, bashin da ake bin Girkar zai ragu da kimanin dala biliyan dari da arba'in.

Ya kara da cewa dole ne bankunan su kara yawan jarinsu domin yi musu garkuwa daga tafka asara koda kasashen Turai sun gaza iya biyan bashin da suke bin su.

Haka kuma za a kara yawan kudaden da ke cikin asusun ceto tattalin arzikin kasashen nahiyar Turai.

'Shugabanni sun yi farin ciki'

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce ta yi imani matakan da suka dauka za su hana matsalar tabarbarewar tattalin arzikin yankin yaduwa zuwa wasu kasashe da ke da karfin tattalin arzki na duniya, irinsu Amurka.

Shi ma shugaban majalisar Turai, Herman Van Rompuy, cewa ya yi matsalar tabarbarewar tattalin arzikin na barazana ga yankin don haka dole ne a shawo kan ta.

Ya ce:''Wannan mataki ya wadatar wajen kare mu daga fuskantar tsaiko.Ina godiya(ga shugabannin Turai) ganin yadda aka ninka kudaden da ake ajiyewa a asusun da ke farfado da tattalin arzikin Turai har sau biyar''.

A nasa bangaren Firaministan Girka, George Papandreou, ya yabawa matakan, yana mai bayyana su da cewa wata sabuwar rayuwa ce ga kasarsa wacce ke fama da basuka.