Ana aikin zakulo mahakan gwal a Zamfara

Masu hakar ma'adinai a jahar Zamfara da ke arewacin Najeriya na ci gaba da kokarin zakulo wasu abokan aikinsu akalla hudu, wadanda wata mahaka ta rufta da su yau mako guda kenan.

Masu aikin ceton, wadanda ke amfani da kayan aiki na hannu kamar magirbi da shebur, sun ce har yanzu suna cike da fatar samun abokan aikin nasu a raye.

Sun dakatar da aikin ceton a baya, bayan da suka jin wani wari na fitowa daga mahakar, abin da ya sa suka yi zaton sun mutu.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Bagega mai tazarar kimanin kilomita 120 daga babban birnin jahar, watau Gusau.

Kwamishinan 'yan sandan jahar ya shaidawa BBC cewa, suna kokarin samun agaji domin kaiwa mutanen dauki.