Shugaban asusun Turai na tattaunawa da China

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Totocin Tarayyar Turai

Shugaban asusun ceto tattalin arzikin kasashen da ke amfani da kudin euro ya fara tattaunawa da jami'an gwamnatin China inda ya ke neman kasar ta zuba jari a Turai.

Mr Klaus Regling ya ce ana samun ci gaba a tattaunawar kuma nan gaba kadan zai sani ko China za ta zuba jari a asusun.

Akwai alamun da ke nuna cewa China za ta zuba kusan dala biliyan dari a asusun.

Shugabannin kasashen da ke amfani da kudin euro na shirin bunkasa asusun zuwa sama da dala tiriliyan daya.