Fiye da 'yan Najeriya dari biyu ne suka dawo daga Libya

Hakkin mallakar hoto System
Image caption Taswirar Najeriya

Hukumar shige-da-fice ta Najeriya ta ce 'yan kasar su dari biyu da hamsin sun dawo daga kasar Libya ta kan iyakar Najeriya da Chadi.

Babayo Alkali, shi ne babban jami'in shige-da-fice a jihar Barno, ya shaidawa BBC cewa hukumar ta tantance mutanen don ganin basa dauke da makamai kafin ta bar su su shigo Najeriya.

Ya kara da cewa ana sa ran wasu mutanen da dama na kan hanyarsu ta dawowa Najeriya daga Libya.

Kafin rikicin kasar ta Libya dai, 'yan Najeriyar da ma wasu kasashen Afurka da dama ne ke ci- rani a kasar ta Libya, kuma da dama daga cikinsu sun taho gida yayin da rikici ya barke a Libyan.