Hukumar NFF zata daddale makomar Siasia

Hukumar wasan Kwallon kafa ta Najeriya, NFF na yin taro kan wani rahoton da kwararrunta suka mika mata dangane da rashin katabus din da kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar , Super Eagles ta yi a gasar cancantar kaiwa gasar karshe na wasan cin kofin kwallon kafa na Afrika a Equitorial Guinea da Gabon.

Mai horadda yan wasan na Najeriya,Samson Siasia, na cikin matsi tun bayan da Najeriyar ta kasa kai wa gaci a gasar.

Yanzu haka wasu na ganin kungiyar ta NFF ta ci moriyar ganga zata yar da kwaure, bayan da aka ce tuni wasu suka fara nuna sha'awar maye gurbin Siasia