Rigakafin shan inna a Niger

A jamhuriyar Nijar yau ne aka soma wani zagayen riga kafin cutar shan inna da za a ci gaba da shi har zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba mai kamawa.

Yara tun daga haihuwa ne har ya zuwa shekaru 5, kimanin miliyan 5 ake sa ran yi wa riga kafin a ko'ina cikin kasar .

A wannan karo dai,shiri ne na hadin guiwa da wasu kasashe makwabtan kasar ta Nijar wadanda bincike ya nuna cewar cutar na dada yin barazana a cikinsu .