Saif al Islam na iya mika kansa ga ICC

Saif al-Islam Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan marigayi kanal Gaddafi

Kotun hukunta manyan laifuka dake birnin Hague ta ce an tuntube ta a madadin dan marigayi Kanal Gaddafi, wato Saiful Islam.

Anyi imanin cewa Saiful Islam na son ya mika kansa ga kotun.

A wata sanarwa da ya fitar, babban mai gabatar da kara na kotun Luis Moreno Ocampo yace idan saiful Islam ya mika kansa, kotun zata saurarreshi kuma za'a bashi damar kare kansa.

Ranar alhamis, an ruwaito wani jami'in Nijar yana cewa Saiful Islam yana kusa da iyakar kasar Nijar da Libya, inda wasu azbinawa ke masa goma ta arziki.