Najeriya ta kori Samson Siasia

Samson Siasia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Siasia ya fuskanci matsin lamba tun bayan wasan Najeriya da Guinea

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta kori kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Super Eagles Samson Siasia daga mukamin sa.

Sanawar sallamar Siasia ta zone ne bayan wani taron da hukumar ta gudanar a ranar Juma'a a Abuja, don tantance matsayin kocin tun bayan da Najeriya ta gaza samun cancantar shiga gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika da za a yi badi a kasashen Gabon da Equatorial Guinea.

Hakan dai ya zo ne bayan da kwamitin kwararru na NFF ya bayar da shawarar a kori kocin.

Siasia ya fuskanci matsin lamba bayan da Super Eagles ta kasa halartar gasar cin kofin kasashen Afrika.

Makonni uku da suka wuce ne Super Eagles ta gaza halartar gasar a karon farko tun shekarar 1986 da aka yi a kasar Masar.

A baya Siasia, mai shekaru 44, ya yi farin jini bayan da ya jagoranci tawagar matasan kasar zuwa wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 a 2005, da kuma wasan karshe na gasar kwallon kafa ta Olympics a 2008.

Amma ya fuskanci matsala bayan da Super Eagles ta tashi 2-2 a wasan da ta kara da Guinea a Abuja - a wasan da take bukatar nasara domin samun damar shiga gasar da za a yi Gabon da Equatorial Guinea.

Rahotanni a kafafen yada labarai na cikin gida na cewa akwai yiwuwar tsohon kyaftin din kasar Stephen Keshi ya maye gurbinsa a matsayin kocin riko.

Sai dai Hukumar ta NFF ta ce sai a ranar Talata ne kwamitinta na kwararru zai gana domin ya bata shawara kan wanda ya kamata ya maye gurbin na Siasia.

Karin bayani