Tarzoma ta barke a Tunisia

Hakkin mallakar hoto Afp
Image caption Masu tarzoma a Tunisia

Tarzoma ta barke a garin Sidi Buzid da ke tsakiyar kasar Tunisia inda wasu mutane da ke goyon bayan wata jam'iya suka ce hukumar zaben kasar ta soke zabe a yankunan da suka samu nasara.

Garin Sidi Buzid dai anan ne aka soma gudanar da juyin-juya-halin da ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin Shugaba Zaine al-Abidina Ben Ali a watan Janairun da ya gabata.

'Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa mutanen da ke gudanar da tarzomar.

Ana zargin jam'iyyar ce da amfani da kudi ba bisa ka'ida ba a lokacin da ake gudanar da yakin neman zabe.