Ayyukan kasa da kasa na fuskantar hadari a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin kasar Faransa masu tabbatar da zaman lafiya a Afghanistan

Wani rahoto da sashen kula da tsaro na Amurka ya fitar ya ce ayyukan kasa da kasa a kasar Afghanistan na cikin hadari daga kungiyoyi masu tada kayar baya daga makwaciyar kasar Pakistan.

Hukumar tsaro ta Pentagon dai ta ce an inganta harkar tsaro sosai a kasar, kuma hare-haren da kungiyar Taliban ke kaddamarwa ya ragu mattuka.

Sai dai rahoton ya yi nuni da cewa akwai wadanda suke kafan angulu da ci gaban da ake samu a kasar.

Ma'aikatar tsaro ta Pentagon dai na wallafa rahoto sau biyu a shekara domin nazarin irin ayyukan da ake gudanarwa a kasar Afghanistan.

Wannan rahoton da ma'aikatar ta wallafa dai na nuni da cewa an samu ci gaba a kasar ta fannin tsaro inda har ma aka mikawa jami'an tsaron Afghanistan ikon wasu wurare a kasar domin tafiyar da al'amuran tsaro.

Har wa yau wadanda su ka rubuta rahoton sun ce akwai wuraren da ke kan iyaka da kasar Pakistaan da ke cikin matukar hadari, saboda masu tada kayar baya, za su iya ja da baya su kuma kara samo makamai.

An dai zargi jami'an tsaron Pakistan da samarwa masu tada kayar baya mafaka, kuma ba sa taka rawar gani wajen murkushe ayyukan ta'addanci.

Rahoton ya ce ba'a wani yunkurin sa'ido kan kayayyakin da ake hada bam da su daga Pakistan, kuma gwamnatin kasar Afghanistan ba ta da kwarewar gudanar da irin wadannan ayyuka.

Rahoton ya kammala da cewa wannan babban koma baya ne, ga sojojin kasa da kasa a kasar ta Afghanistan.

A siyasance dai wannan ba zai yiwa shirin yakin neman zaben shugaba Obama da za a yi a badi dadi ba.

Shugaban Amurkan dai ya nanata cewa zai dawo da dubban sojojin Amurka da ke Afghanistan a watan Satumban shekara ta 2012.

Har wa yau ya ce za'a dawo da dubban sojojin kasar da za su rage zuwa gida a shekara ta 2014.