Kasashen larabawa sun yi Allah-wadai da Syria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kungiyar kasashen larabawa ta nemi a kare fararen hula

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun aike da wani sakon kar-ta-kwana ga Shugaba Bashar al Assad na Syria suna Allah wadai da ci gaba da kisan fararen hular da ke zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa.

Minstocin sun yi kira ga Mista Assad ya dauki dukkan matakan da suka wajaba don kare farraren hula.

Kiran ya zo ne a daidai lokacin da aka kara samun tashe-tashen hankula a kasar ta Syria.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sunce akalla fararen hula 37 ne aka kashe bayan masu zanga zanga sun fantsama a tituna suna bukatar a sanyawa kasar haramcin zirga-zirgar jiragen sama.

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin Bil Adama ta Syria ta ce an yi zanga zanga a Homs da Qamishly a arewa da kuma Deraa a kudanci.

Haka kuma akwai rahotanni na yin artabu a Hama tsakanin yan adawa da dakarun tsaroGwamnati ta zargi kungiyoyin masu daukar makamai da kai hari a kan Ofishin yansanda a Homs.

Ba dai san ainihin dalilin mace - macen ba, kuma ba abu ne mai saukin tantance rahotanin ba saboda Syria ta saka takaici mai tsauri a kan kafofin watsa labarai.