Karar fashewar wani abu a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na cewa an ji karar fashewar wani abu mai karar gaske da ake zaton Bom ne.

Rundunar hadin-gwiwar jami`an tsaro a jihar ta ce abin ya fashe ne da misalin karfe Takwas da rabi na safe, amma lamarin bai ritsa da kowa ba kuma nan take aka tsare wasu mutane biyu da ake zargin su ne suka kai harin. Sai dai wasu mazauna birnin kamar yadda rahotanni suka ce na zargin cewa an kai harin ne kan jami`an tsaron amma kuma jami'an tsaro sun ce ba haka lamarin yake ba

Wa'adi

Wannan harin bom din dai ya zo ana saura kwana daya wa`adin da rundunar tsaron ta bai wa al`umar birnin na Maiduguri cewar duk wani da ke da makami a hannunsa ya mika wa hukuma, tana mai tabbatar da cewa ba za a hukunta shi ba idan ya yi hakan a cikin lokacin da aka kebe.

Sai ta yi gargadin cewa daga goben, jami`an tsaron za su fara bincike na musammman, kuma duk wanda aka kama da makami za a hukunta shi.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu wanda ya yi ikirarin kai wannan hari na baya-bayan nan.