NATO ta kawo karshen ayyukanta a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters

A yau ne aka shirya kawo karshen hare hare da jiragen samar da suka taimaka wajen hambarar da Kanar Muammar Gaddafi daga kan karagar mulki a Libya.

Tuni dai kungiyar kawance ta NATO ta dakatar da kai hare-haren, kuma nan bada jimawa ba zata kawo karshen shirin nan na tabbatar da hana zirga zirgar jiragen sama a sararin samaniyar kasar ta Libya.

Hukumar wucin gadin Libya ta bukaci kungiyar tsaron NATO da ta cigaba da baiwa kasar taimako ta fuskar tsaro.

Kakakin ma'aikatar tsaron Libya, Kanar Ahmed Bani, ya ce ko da yake har yanzu ba'a san inda dan Kanar Gaddafi, Saiful Islam yake ba, amma kuma kasar zata iya yin ayyukanta kamar yadda take bukata ko da bata samun taimakon daga jiragen NATO