Taliban ta dauki alhakin harin Kabul.

Kungiyar Taliban ta ce ita keda alhakin wani harin kunar bakin wake da aka kai birnin Kabul na Afghanistan, wanda ya yi sanadiyyar hallaka dakarun Amurka 13 da kuma fararen hula da dama.

Wani dan kunar bakin wake ne cikin motar sa shakare da nakiyoyi ya karawa wata motar safa dake dauke da sojojin.

Nan take harin yayi ajalin sojojin Amurka 13.

Ba kasafai irin wannan harin ke hallaka sojojin dadama haka ba.

A Kalla farar hula ukku ne da kuma wani dan sandan Afghanistan suka mutu a lamarin.

Anji karar harin a kusan ko ina a Kabul.

Tuni kungiyar taliban ta dauki alhakin kitsa harin, kuma 'yan sanda sun killace wurin da lamarin ya faru.