Kotu ta ce ma'aikatan Qantas su koma aiki

Hakkin mallakar hoto PA

Wata kotu mai zaman kanta dake sauraren kararrakin da suka shafi kwadago a Australia, ta umarci ma'aikatan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Qantas da su kawo karshen yajin aikinsu, wanda ya kai kamfanin ga dakatar da tashin duka jiragensa.

Alkalai ukkun da aka nada dan yanke hukunci akan wananan takaddama sun ce dole ne kungoyiyon kwadago su kawo karshen yajin aikin da maiakatan komfanin Qantas din ke yi.

Wajibi ne dai a yi aiki da hukuncin, wanda alkalai 3 suka yanke.

Afuwa

Shugaban kamfanin na Qantas, Alan Joyce, ya ce mai watakila jiragen kamfanin su fara dan kwarya-kwaryar tashi daga gobe Litinin da maraice . Mr Joyce ya kuma nemi afuwa ga fasinjoji kusan dubu 70 da yajin aikin shafa a duk fadin duniya.

Hukuncin dai shine mafitar da komfanin Qantas din yace zai bashi zarafin komawa aiki.

Fiye da jirage 100 ne aka takatar a sa'o'i 36 da suka wuce sakamakon yajin aikin.

Kawo yanzu babu tabbaci daga komfanin akan ko yaushe jiragensa zasu tashi.