Dattawan Benue sun koka da matsalar tsaro

Image caption Taswirar Najeriya

A Jihar Benue da ke arewacin Najeriya, wasu dattawa ne ke kokawa da yadda suka ce, al'amarin tsaro na tabarbarewa a jihar.

Dattawan sun ce, a kwanakin nan kimanin mutane biyar sun mutu a wani rikicin siyasa.

Dattawan dai sun yi zargin cewa gwamnatin jihar ce ke kitsa wasu rigingimun da nufin murkushe 'yan adawa.

Suna masu fargabar cewa idan gwamnatin tarayya ba ta taimaka ba to lamarin zai munana.

Sai dai gwamnatin jihar a nata bangaren ta musanta zargin, tana mai cewa abokan adawa ne kawai ke kokarin bata mata suna.

Sanata Joseph Waku, wanda ke daya daga cikin dattawan ya ce gwamnatin jihar na yin hakan ne da nufi murkushe 'yan adawa.

Ya ce; " Jam'iyya mai mulki a jihar ba ta bar jam'iyyun adawa sun tafiyar da al'umuransu, inda take tsare 'ya'yansu da dama."

Senata Waku ya ce dolene, gwamnatin tarraya ta sa baki kada al'amarin ya jefa jihar cikin wani yanayi na tashin hankali.