Shugaban hukumar zaben Liberia ya ajiye aikinsa

Hakkin mallakar hoto google
Image caption James Fromayan, ya ajiye aiki ne saboda zargin da 'yan adawa su ka yi masa

Shugaban hukumar zabe ta Liberia ya ajiye aikinsa ana sauran kusan mako guda a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

Shugaban hukumar, James Fromayan, ya ce ya yi murabus ne saboda a zauna lafiya.

Babbar jam'iyyar adawa ta Congress for Democratic Change, CDC, wadda tai zargin cewa an tafka magudi a zagayen farko na zaben, ta zargi Mista Fromayan da karkata ga wani bangare.

Dan takarar jam'iyyar, Winston Tubman ne zai kalubalanci shugaba mai ci, Ellen Johnson Sirleaf, a zagaye na biyu na zaben.