Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Rawar da kungiyoyi ke takawa a fagen lafiyar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Medecins Sans Frontieres na daga cikin manyan kungiyoyin lafiya na duniya

Inganta lafiyar yara 'yan kasa da shekaru biyar da ta mata masu juna biyu na daga cikin muradun karni na majalisar dinkin duniya, wanda ake son cimmawa nan da shekarar 2015.

Yawaitar mace-macen yara da kuma mata masu juna biyu, na daga cikin dalilan da suka sanya Shugabannin kasashen duniya kudirta aniyar rage yawan mace macen da akalla kashi uku bisa hudu.

Musamman ganin cewa za'a iya gujewa da dama daga cikin abubuwan dake janyo salwantar rayuka, tare kuma da tabbatar da cewa sun samu kulawar da ta kamata ta bangaren lafiya.

Alamu dai na nuni da cewa an samu gagarumar nasara a wannan bangare, duk da dai cewa akwai wuraren da har yanzu ke can baya.

Daga shekarar 1990 zuwa 2008, yawan yara 'yan kasa da shekaru biyar dake rasuwa a kullum a duniya ya ragu da kimanin dubu goma a kowacce rana.

Sai dai har yanzu akwai sauran rina a kaba musamman a kasashen yamma da sahara dake nahiyar Afrika inda cikin kowanne yara shida da ake haifa, akalla daya na rasuwa a kafin cikar shekaru biyar da haihuwa, kuma cikin yara fiye da miliyan takwas da suka rasu a duniya a tsakanin shekarun, rabin adadin daga wannan yanki suke.

Ciwuka hudu ne da manyan hukumomin lafiya na duniya suka bayyana kan cewa su suka fi yawan salwantar da rayukan yara 'yan kasa da shekaru biyar da suka hada da Numonia da amai da gudawa da zazzabin cizon sauro da kuma AIDS ko Sida.

A bangaren mata masu juna biyu, matsaloli da suka hada da zubar jini da ya wuce kima da kuma hawan jini, sune ke sanadiyyar salwantar da rayukan akalla rabin adadin mata masu juna biyun dake rasuwa a duk shekara.

Dabarun Sakatare janar na majlisar dinkin duniya, Ban ki-moon kan kiwon lafiyar mata da yara da aka fitar a shekarar 2010 ya nuna cewa kowa na da muhimmiyar rawar da ya kamata ya taka wajen inganta kiwon lafiyar mata da yara.

Ya fara ne da ambato gwamnatoci da 'yan majalisa a matakai daban daban a duniya da cewa dole su bada fifiko a harkan kiwon lafiya, su kuma amince da kara yawan kudade domin aiwatar da ayyuka a wannan fanni, tare kuma da tabbatar da cewa an yi amfani da kudaden ta yadda ya dace.

Su ma kungiyoyi masu zaman kansu a cewa Mr. Ban na da muhimmiyar rawa da za su taka, inda ya ce ya zama dole su bi diddigin yadda ake aiwatar da ayyuka sau da kafa tare da tabbatar da cewa dukkan masu ruwa da tsaki sun yi abin da ya kamata.

Sannan kuma ya zama dole su zage damtse wajen fafutuka janyo hanakali da wayar da kai tare kuma da kara zuba suma nasu kudaden domin inganta lafiyar mata da yara.