Hukumar Unesco ta amince da Falasdinawa

unesco Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Kasashe 107 ne suka goyi bayan Falasdinu

Hukumar kyautata ilimi da kimiya da al'adu ta majalisar dinkin duniyar, ta amince da Hukumar Falasdinu a matsayin cikakkiyar mamba duk adawar Amurka da Isra'ila.

Matakin shi ne na baya-baya a kokarin da Hukumar Falasdinun ke yi, na ganin an amince da ita a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Kashi biyu bisa ukku ne na kasashen da suka kada kuri'a, suka yarda a shigar da Falasdinawan a cikin Hukumar ta UNESCO.

Daga cikin kasashe 173 da ke da 'yancin kada kuri'a, 107 ne suka goyi bayan Falasdinu, inda 14 suka nuna adawa, sannan 52 suka kaurace.

Kafin a kada kuri'ar, Amurka ta ce za ta daina bayar da tallafi ga Hukumar ta Unesco, idan aka amince da bukatar ta Falasdinawa.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a a watan Nuwamba kan ko zai amince da Falasdinu ta zama cikakkiyar kasa a Majalisar, sai dai Amurka ta ce za ta hau kujerar naki.

Samun kujera a Unesco - za a iya yi masa kallon wani kwarya-kwaryar mataki ne na samun 'yancin kai, a cewar wakilin BBC Jon Donnison, a birnin Ramallah.

'Ba za ta kawo sauyi a kasa ba'

Amma Falasdinawa na yi masa kallon wani bangare na yunkurin da suke yi na samun amincewar kasashen duniya da kuma matsa lamba kan Isra'ila.

Wannan ita ce Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta farko da Falasdinawa suka nemi shiga tun bayan da suka gabatar da bukatar kasancewa cikakkiyar mamba ga Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba.

"Wannan kuri'ar za ta rage wani kankanin adadi na cin zarafin da ake yi wa al'ummar Falasdinawa," kamar yadda ministan harkokin wajen Falasdinawa Riyad al-Malki ya shaida wa taron Unesco a birnin Paris, bayan bayyana sakamakon.

Sai dai Isra'ila ta yi Allah wadai da matakin, tana mai cewa ba zai sauya komai ba kan matsayinta a kan Falasdinawa.

"Isra'ila ta yi watsi da matakin da babban taron UNESCO ya dauka a ranar 31 ga watan Oktoba, na amince wa da Falasdinawa a matsayin mamba ta Hukumar," a cewar sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila.

"Wannan wata dabara ce ta Falasdinawa su kadai, wacce ba za ta kawo sauyi a kasa ba, sai dai za ta kawar da damar da ake da ita ta komawa fagen tattaunawa."