Amurka ta daina ba UNESCO tallafi

Amirka ta dakatar da gudunmawar kudaden da take ba hukumar kyautata ilimi da kimiya da al'adu ta majalisar dinkin duniya, watau UNESCO, bayan da hukumar ta amince da Hukumar Falasdinu a matsayin cikakiyar mamba.

Ma'aikatar harkokin wajen Amirkan ta ce, Amirkan ba zata zubawa UNESCOn dala miliyan sittin ba a watan Nuwamba, kamar yadda aka tsara.

Kashi biyu bisa ukku ne na kasashen da suka kada kuri'a, suka yarda a shigar da Falasdinawan a cikin UNESCOn, duk da adawar da Amirka da Isra'ila ke nunawa.