Boko Haram ta ce ita ta kai harin Damaturu

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Kungiyar nan da aka fi sani da suna Boko Haram a Najeriya ta ce ita ce ta kai wadansu jerin hare-hare a arewa maso gabshin kasar, inda akalla mutane sittin da biyar suka rasa rayukansu.

Wadansu rahotanni dai sun ce yawan wadanda suka mutu ya kai dari.

Wani jami'in kungiyar agaji ta Jama’atu Nasril Islam a garin Damaturu ya shaidawa BBC yawan gawarwakin da suka samu:

“[Gawarwaki] casa’in da shida [muka kwaso], dukkansu kuma sun mutu.

“Akwai Musulmi, da Kirista, da jami’an tsaro; duka gawarwakin a [gauraye suke]—haka muka debo muka kawo”.

Wani mai magana da yawun kungiyar ta book Haram ya ce za a kai wasu karin hare-haren.

Kusan daukacin wadanda suka rasa rayukasn nasu sun mutu ne a garin Damaturu, inda wani dan kunar bakin wake ya kai hari a kan hedkwatar rundunar 'yan sanda ta garin.

An kuma kai hare-hare da gurneti a kan wasu majami'u.

Tashin hanakalin dai ya fara ne daga birnin Maiduguri, inda wasu 'yan kunar bakin wake suka farwa wani sansanin soji ranar Juma'a.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce ya damu matuka da kai hare-haren, musamman ma ganin ya faru ne a lokacin hidimomin salla.

Shugaba Jonathan, wanda ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawunsa, Reuben Abati, ya kuma ce gwamnati ta kuduri aniyar ganin an hukunta wadanda ke da hannu a al'amarin; sannan ya ce ya fasa wata tafiya zuwa jiharsa ta asali, Bayelsa, don halartar bikin auren wani dan uwansa, saboda faruwar al’amarin.

Karin bayani