An samu likitan Michael Jackson da laifi

Dokta Conrad Murray Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dokta Conrad Murray

Masu taimakawa alkali yanke hukunci sun samu tsohon likitan Michael Jackson, Conrad Murray, da laifin aikata kisa ba da niyya ba.

An dai zargin likitan ne mai shekaru hamsin da takwas da haihuwa, da yin watsi da Michael Jackosn din bayan ya ba shi adadin da ya wuce kima na maganin propofol wanda ake amfani da shi yayin tiyata.

Hawaye ya zubowa mahaifiyar Michael Jackson din, Katherine, lokacin da ta ji wannan hukunci a cikin kotun, yayin da a waje kuma masu kaunar mawakin suka barke da sowa.

Alkalin ya bukaci a ci gaba da tsare Dokta Murray har zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba, lokacin da za a yanke masa hukunci zaman kaso.