An bayyana sakamakon zaben Guatemala

Otto Perez Molina Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Otto Perez Molina

Wani tsohon hafasan soja ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a Guatemala.

Bayan kidaya kusan dukkan kuri'un da aka kada, hukumar zabe ta kasar ta bayyana Otto Perez Molina a matsayin wanda ya lashe kusan kashi hamsin da biyar cikin dari na kuri'un.

Mista Perez Molina ne dai zai kasance tsohon jami'in soja na farko da zai jagoranci kasar tun bayan yakin basasar da ya zo karshe a shekarar 1996.

Sai dai jami'an zabe sun bayyana cewa kasa da kashi hamsin cikin dari na masu zabe ne suka kada kuri'a.

Wani jami'in zabe mai suna Nelson Donis ya bayyana cewa, “Mun sa rai mu ga masu zabe sun fito sosai amma wadanda suka kada kuri'a wannan karon ba su kai yawan na zagayen farko na zaben ba”.

A Nicaragua kuwa, Yayin da ake ci gaba da kidaya kuri'u bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, shugaban kasa mai ci, Daniel Ortega, ne ke kan gaba.

Mista Ortega dai na fatan yin mulki ne a karo uku.

Babban abokin hamayyarsa dai wani fitaccen ma'aikacin gidan radio ne mai ra'ayin mazan jiya, Fabio Gadea.

An dai fara zaben Mista Ortega ne a shekarar 1979.

Bayan ya sha kaye a zaben 1990 kuma aka sake zabensa a shekarar 2006.

Sai dai kuma abokan adawarsa na zarginsa da muzgunawa 'yan adawa da kuma yin amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba.