'Yan adawa na gangami a kasar Italiya

Firayim Minista Silvio Berlusconi na Italiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Firayim Minista Silvio Berlusconi na Italiya

Dubban magoya bayan 'yan adawa sun yi gangami a tsakiyar birnin Rome, inda suke kira ga Firayim Ministan Italiya, Silvio Berlusconi, ya yi murabus.

Jagoran jam'iyyar Democratic Party, Pierluigi Bersani, ya shaidawa gungun mutanen da suka taru a dandalin Piazza San Giovani cewa a shirye ya ke ya jagoranci wata sabuwar gwamnati tare da sauran jam’iyyun adawa.

Gwamnatin Mista Berlusconi dai na fuskantar karin matsin lamba ne saboda dimbin bashin da ake bin kasar ta Italiya.

A makon da ya gabata ma dai wasu ‘yan Majalisar Dokokin Italiya su shida wadanda ke dasawa da Mista Berlusconi a da sun yi kira gare shi ya yi murabus.