Firayim Ministan Italiya na fuskantar jarrabawa

Firayim Ministan Italiya, Silvio Berlusconi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Firayim Ministan Italiya, Silvio Berlusconi

Firayim Ministan Italiya, Silvio Berlusconi, zai fuskanci wata muhimmiyar jarrabawa a majalisar dokoki yau Talata, yayinda kasar ke fafutukar ganin ta kaucewa fadawa irin matsalar da Girka ta afka.

Majalisar dai za ta kada kuri'a ne a kan kasafin kudin kasar; hakan kuma zai nuna ko Mista Berlusconi ya yi asarar goyon bayan da gwamnatinsa ke samu a majalisar.

Ana dai ci gaba da nuna damuwa da yadda matsalar tattalin arzikin da ta addabi kasashen da ke amfani da kudin euro ke barazana ga kasar ta Italiya, wadda ita ce ta uku mafi karfin tattalin arziki a yankin.

Mista Berlusconi dai ya tsallake rijiya da baya yayin kada kuri'un yanke kauna har sau hamsin, ya kuma yi watsi da hasashen da ake cewa mai yiwuwa a tilasta masa yin murabus.

Damuwar da ake nunawa a kan matsalar kasar ta Italiya ta sha gaban abubuwan da ke faruwa a Girka inda shugabannin siyasa ke ci gaba da takaddama a kan kafa wata sabuwar gwamnatin hadin kan kasa wadda za ta aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu.

Karin bayani