Mutane biyu sun mutu a harin gurneti a Kenya

Shugaba Mwai Kibaki da Firayim Minista Raila Odinga na Kenya
Image caption Shugaba Mwai Kibaki da Firayim Minista Raila Odinga na Kenya

Wani harin da aka kai da gurneti a harabar wata majami'a a gabashin Kenya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu ya kuma jikkata wadansu mutanen da dama.

Wani gurnetin kuma wanda aka jefa a kofar wani sansanin sojin da ba shi da nisa daga wurin a garin Garissa bai tashi ba.

'Yan sandan Kenya sun ce suna bincike don gano ko harin na da alaka da kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Islama ta Somaliya, al Shabaab, wadda ta kai hare-hare da dama a Kenya a 'yan makwannin da suka gabata.

A watan da ya gabata ne dai kasar ta Kenya ta tura dakarunta cikin Somaliya don su yaki kungiyar ta al Shabaab wadda ta zarga da sace wasu 'yan kasahen waje.