Obama ya yi kira a yi zaben adalci a Liberia

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Obama na Amurka ya ce kamata ya yi mutanen Liberia su samu zarafin kada kuri'a ba tare da tsoro ba a zaben shugaban kasar zagaye na biyu yau.

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa zaben na cike da tarihi kum awata dama ce ga mutanen Liberia su karfafa tsarin dimokuradiyya.

Dan takarra 'yan adawa Winston Tubman dao zai kauracewa zaben, yana mai cewa ba a cika sharuddan gudanar da sahihin zabe ba.

An bindige akalla mutum guda a Monrovia, babban birnin kasar, yayin wani gangami na 'yan adawa jiya Litinin.

Mataimakin shugaban 'yan adawar, tsohon dan wasan kwallon kafa George Weah ya yi kira a dage zaben, yana mai cewa:

"Muna cikin wani gangami na lumana dauke da kyallaye da kwalaye masu dauke da sakon a yi adalci, a bi hanyar tabbatar da dimokuradiyya, sai kwatsam aka fara jefo mana hayaki mai sa hawaye".