An sake samun tashin hankali a Homs, Syria

Shugaban Syria, Bashar al-Assad Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Syria, Bashar al-Assad

An bayar da rahoton cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a wadansu sababbin hare-haren da dakarun tsaron Syria suka kai ranar Asabar a birnin Homs.

An ci gaba da tashin hankali ne dai duk da amincewar da gwamnatin kasar ta Syria ta yi a farkon makon da ya gabata ta janye dakarunta ta kuma hau teburin shawarwari da 'yan adawa kamar yadda wani shirin samar da zaman lafiya na kungiyar kasashen Larabawa ya tanada.

Kungiyar ta kasashen Larabawa ta ce rashin nasarar shirin nata ka iya jawo wani babban bala'i.

A nasu bangaren, hukumomi a kasar ta Syria sun ce sun saki mutane dari biyar da hamsin da uku wadanda aka kama yayin zanga-zangar kin jinin gwamnati don murnar babbar salla.

Karin bayani