An zargi dan takarar shugabancin Amurka

Herman Cain
Image caption Herman Cain

Wata mata ta zargi daya daga cikin mutanen da ke fatan yiwa jam'yyar Republican takarar shugabancin Amurka, Herman Cain, da aikata dabi'un da ba su dace ba, lokacin da ta je wurinsa neman shawara.

Matar mai suna Sharon Bialek, ita ce ta hudu da ta yi irin wannan zargi a kan Mista Cain, amma kuma ita ce ta farko da ta yi hakan a kafofin yada labarai.

Ta ce al'amarin ya faru ne a motar Mista Cain a Washington shekaru goma sha hudu da suka gabata.

"Na dauka za mu je ofishinsa ne don ya nuna mini inda ya ke aiki, amma a maimakon haka sai ya ajiye motar tasa can da nisa sannan ba zato ba tsammani ya dora hannayensa a kan kafuwana ta karkashi sket dina".

Ofishin kamfen na Mista Cain ya ce sam babu kamshin gaskiya a wannan zargi.