Kokarin kafa sabuwar gwamnati a Italiya

Shugaban Italiya, Giorgio Napolitano, ya soma tuntubar bangarori dabam dabam, game da kafa sabuwar gwamnati, bayan murabus din Piraminista Silvio Berlusconi, jiya Asabar.

Wani masanin tattalin arziki da ake mutuntawa sosai, Mario Monti, shine ake kyautata zaton zai shugabanci sabuwar gwamnatin, wadda za ta hada kwararru.

Babban aikin da ke gaban gwamnatin da ake jira shine: aiwatar da tsatsauran shirin tsuke bakin aljihun gwamnati, a kokarin da Italiyar ke yi na sauke dimbin bashin da ke kanta:

Wani mazaunin birnin Roma ya ce, yana fatan al'amurra za su kyautatu, to amma suna jira ne su ga kamun ludayin sabuwar gwamnatin da za a kafa.

Ana fatan cewa za a nada sabuwar gwamnatin, kamin a bude kasuwannin kudade a gobe Litinin.