Fafaroma ya yi kira da a kawo karshen tashin hankali a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban fadar Vatican Fafaroma Benedict ya yi kira da a kawo karshen tashe tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, inda kimanin mutane dari suka rasa rayukansu a hare haran bama-bamai da harbe harben da aka kai.

Fafaroma ya ce yakamata a kawo karshen rikicin wanda ba ya warware matsaloli illa ya karasu. Ya ce rikici na kara kiyayya ko da a tsakanin mutanen da sukai imani ne.

A ranar juma'a ce aka samu tsashe tashen bama bamai a a garin Damaturu babban birnin jihar Yobe a arewacin Nigeria, lamarinda ya yi sanadiyar fiye da mutane 60 Kungiyar Islama a Najeriya, da aka fi sani da Boko Haram ta yi ikirarin kai hare hare kan ofisoshin 'yan sanda, da gine ginan gwamnati da kuma coci-coci. Shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan ya ce tilasne a