Jirgin karkashin kasa ya fara aiki a Aljeriya

Aljeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Abdelaziz Bouteflika yana bude tashar jirgin ranar Litinin

An fara jigilar fasinja a jirgin karkashin kasa da aka dade ana jira a birnin Algiers na kasar Aljeriya - wanda shi ne irinsa na biyu a nahiyar Afrika.

Shugaba Abdelaziz Bouteflika shi ne ya bude tashar jirgin ranar Litinin, a wani biki da ya samu halartar daruruwan mutane da suka dade suna son fara aiki da sabuwar hanyar sufurin.

An fara aikin ginin ne shekaru 28 da suka wuce, sai dai ya samu tsaiko saboda matsalar tattalin arziki da kuma yakin basasar da aka shafe shekaru ana yi.

Jirgin wanda ke da nisan kilomita shida da rabi, yana da tasoshi 10.

Ya hada tsakiyar birnin Algiers da yankin Kouba da ke wajen birnin.

An fara aikin ne a farkon shekarun 1980, amma faduwar farashin mai da gas a duniya ya jefa tattalin arzikin kasar cikin mummunan hadari.

Jama'a na korafi kan farashi

Aljeriya ce kasa ta hudu a duniya da tafi arzikin iskar gas.

A shekarun 1990, kasar ta fada yakin basasa inda dakarun gwamnati suka fara yakar kungiyoyin Islama masu dauke da makamai.

Akalla mutane 250,000 ne suka rasa rayukansu.

Ana hasashen cewa an gina jirgin kasan ne a kan dinare biliyan 90 na kasar (sama da dalar Amurka biliyan daya).

Za a rinka biyan dinare 50 kan kowacce tafiya - farashin da yawancin 'yan Aljeriya ke korafi a kai.

Jirgin karkashin kasa na farko da ake da shi a nahiyar Afrika shi ne na birnin Alkahira na kasar Masar.