Kotu ta tabbatar da zaben Goodluck Jonathan

CPC
Image caption Jam'iyyar CPC ce ta zo ta biyu a zaben na watan Afrilu

Kotun daukaka kara a Najeriya ta yi watsi da karar da jam'iyyar CPC ta shigar tana kalubalantar zaben shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP.

Duka alkalan kotun guda biyar sun amince wajen tabbatar da zaben da aka yi wa Jonathan a ranar 16 ga watan Afrilu, sannan ta yi watsi da kiran da jam'iyyar adawa ta CPC ta yi na a soke zaben a wasu sassan kasar.

An bayyana Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaben 16 ga watan Afrilu da kashi 59 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Sai dai mutumin da ke binsa a zaben, janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC, wanda ya samu kashi 32 cikin dari ya ki amince wa da sakamakon zaben.

A don haka ne jam'iyyar ta sa ta Congress for Progressive Change (CPC) , ta shigar da kara domin kalubalantar zaben a watan Mayu.

Alkalai biyar ne suka yi zaman karkashin jagorancin mai shara`a Kumai Biyang Akaahs, wanda bayan ya kwashe sama da sa`o`i biyu yana jawabi a kan bukatun da bangarorin masu kara da masu kariya suka gabatar kana yanke hukunci.

'Zama bai same mu ba'

Hukuncin da baki dayan alkalan suka yi ittifaki a kai, cewar jam`iyyar CPC ta gaza wajen kafa hujjoji masu gamsarwa da za su tabbatar da zargin da ta yi cewar an tabka magudi a zaben shugaban kasar da ya gabata.

Daga cikin shaidu sama da arba`in da jam`iyyar ta gabatar, kotun ta ce ba daya daga cikinsu da ta gamsu da bayanansa, don haka ne ta yi watsi da karar.

Sakataren jam'iyyar CPC na kasa Injiniya Buba Galadima, ya shaida wakilin BBC Ibrahim Isa cewa zama bai same su ba:

"Tun kafin mu iso kotu mun san abinda zai faru.

"Za mu daukaka kara, za mu tabbatar cewa mutanen duniya sun son ko ana adalci a Najeriya ko ba a yi".

Buba Galadima ya kuma kara da cewa ba sa yin nadamar zuwa kotun ko kadan.

Sai dai ana ta bangaren jam'iyyar PDP, ta bakin mai magana da yawunta Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali, cewa ta yi ba ta yi mamakin hukuncinba, saboda ba ta sabawa ka'ida wajen zaben ba:

"Saboda mun san cewa PDP ta yi aiki sosai, ba jihar da ba muje mun yi aiki ba, kuma mun san a kwai alkalai kwararru masu adalci a Najeriya".

Ya kuma kara da cewa ba sa tsoron jam'iyyar CPCn ta daukaka kara, domin suna fatan samun nasara a kodayaushe.

A yanzu dai zabi daya ne ya rage ga jam`iyyar CPCn ta fuskar shari`a, wato tana da damar daukaka kara zuwa kotun kolin kasar, wadda daga ita sai dai a dangana.

Karin bayani