Ana ci gaba da muhawara kan janye tallafin mai a Najeriya

A Najeriya, wata kungiya mai zaman kanta, Initiative for Peace, and Industrial Harmony, ta gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki a kan batun shirin da gwamnatin kasar ke yi na janye tallafin da take baiwa bangaren man fetur a kasar.

Wannan batu dai ya haifar da zazzafar mahawara a cikin kasar, kuma tuni kungiyoyin kwadago suka ce ba za su amince da shi ba.

Sai dai a nata bangaren, gwamnatin Najeriyar cewa take za a yi amfani da kudin tallafin wajen inganta rayuwar talaka.

A ci gaba da muhawara kan wannan batu na janye tallafin mai a Najeriya,wata kungiya ta mabiya addinin kirista mai suna Concerned Northern Christian Association ta nuna damuwa game da shi.

Kungiyar ta ce cire tallafin man fetur, ba alheri ba ne ga 'yan kasar, bisa la'akari da matsalolin da zasu haifar ga jama'a.

Kungiyar har ila yau ta kara nuna damuwa a bisa abinda ta ce goyon bayan da shugaban kungiyar CAN na kasa Pastor Ayo Oritsejafor ya nuna bisa shirin na gwamnatin tarayya na cire tallafi.

Ta ce bisa la'akari da matsalolin da shirin zai haifawa jama'a, bai kamata wani shugaba ya goyi bayan shirin ba.