Kotu ta yi watsi da karar da CPC ta shigar

A Najeriya, kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da karar da jam`iyyar adawa ta CPC ta shigar, inda ta kalubalanci zaben da aka yi wa Dr Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasa.

Kotun ta ce jam`iyyar CPC ta gaza wajen kafa hujjoji masu gamsarwa da za su tabbatar da cewa an tabka magudi a zaben da aka yi wa shugaban kasar da mataimakinsa Architect Namadi Sambo.

A ranar sha takwas ga watan Mayun wannan shekarar ne jam`iyyar CPC ta shigar da karar, ciki har da Jam`iyyar PDP mai mulki da Shugaban Hukumar zaben kasar da kuma baki dayan Kwamishinon zaben Najeriya da ke jihohin kasar talatin da shida, da ma Birnin tarayya, Abuja.