Matsalar cin hanci a wasan kwallon kirket

Wasu 'yan wasan kwallon kirket su biyu 'yan kasar Pakistan - tsohon kyabtin din kasar, Salman Butt, da majefin kwallo, Mohammad Asif - dukkansu wata kotu a nan London ta same su da laifin mallakar hannu a abin kunyar da ya shafi caca a kan wasan.

Dukkansu dai sun musanta hannu a kan karbar hanci a lokacin karawar gwaji a nan Ingila a bara - amma juri da ke taimaka wa alkali yanke hukunci, sun yanke shawarar cewa lalle sun shirya yin kuskure wajen jefa kwallon a daidai wurin da aka kulla da su za su yi hakan.

Wani mai gabatar da kara ya ce wannan shari'a manuniya ce ta irin yadda cin hanci da rashawa ya zama tuwon-gadun a wasan kirikit a duniya.