Kotu ta tabbatar da zaben Rabi'u Kwankwaso

Rabi'u Kwankwaso Hakkin mallakar hoto google
Image caption Kwankwaso ya kayar da Salihu Takai ne na jam'iyyar ANPP

Kotun sauraren Korafin zabe dake zama a Kano ta kori karar da dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar ANPP Malam Salihu Sagir Takai ya shigar gabanta yana kalubalantar nasarar da injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya samu a zaben watan Aprilu da ya gabanta.

Dan takarar na jam'yyar ANPP ya yi zargin cewa an tafka magudi yayin zabukan na watan Afrilun bana.

A cewar kotun dai masu shigar da karar basu gabatar da gamsassun shedun da za su iya sa a soke zabenba.

A bangarenta jam'iyyar ta ANPP ta ce sai nan gaba za ta bayyana matsayinta kan hukuncin.

'Yan PDP na murna

Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, ya ce an tsaurara matakan tsaro a cikin da waje da kuma hanyoyin zuwa kotun.

Rahotanni sun kuma ce kotun ta cika makil da magoya bayan bangarorin biyu da kuma 'yan jarida.

Wakilin na mu ya kuma ce magoya bayan jam'iyyar PDP sun bazama a cikin gari inda suke ta murna kan hukuncin kotun.

Jama'a da dama dai suna cikin dar-dar kan sakamakon shari'ar abinda ya sanya ma wasu basu bar 'ya'yansu sun je makaranta ba a ranar Talata, saboda gudun abinda ka iya faruwa.

Amma wakilin namu ya ce komai na tafiya kamar yadda aka saba a birnin na Kano.

Karin bayani