Kotu ta amince a mika Assange Sweden

Julian Assange Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Julian Assange ya yi fice da shafinsa na Wikileaks

Wata babbar kotu a London ta ce za'a iya mika mutumin da ya kirkiro shafin intanet mai kwarmata bayanai na Wikileaks Julian Assange zuwa Sweden, domin ya fuskanci shari'a kan zargin fyade da cin zarafin wasu 'yan mata biyu.

Alkalai biyu ne suka yanke hukuncin cewa matakin da kotun farko ta dauka na cewa a mika Assange ya yi dai-dai.

Mahukunta a Sweden na son a mika shi ne domin ya amsa tambayoyi kan zargin yiwa wata mace fyade da kuma cin zarafin wata a birnin Stockholm bara.

Lauyan Mr Assange ya ce za su daukaka kara a kotun koli.

A yanzu suna da kwanaki 14 domin su dauka karar, ta hanyar nuna wa kotun cewa lamarin na da muhimmanci ga jama'a.

A watan Fabreru ne wani alkalin wata karamar kotu Howard Riddle ya yanke hukuncin cewa a mika Mr Assange bayan ya saurari ba'asi a kotun magistiri ta Westminster.

Sai dai dan kasar ta Australia mai shekaru 40 ya musanta dukkan zargin da ake yi masa.

Amma a hukuncin da suka yanke, alkalan babbar kotun sun ce, hanyoyin da aka bi wajen bayar da sammacin kame Mr Assange da abubuwan da suka biyo baya ba su sabawa shari'a ba.

Sun yi watsi da bayanan Assange na cewa sammacin ya fito ne daga mai gabatar da kara ba wai "hukumar shari'a ba".

Karin bayani