An yi jana'izar Janar Saibu a Nijar

A jamhuriyar Nijar yau ne aka yi jana'izar tsohon shugaban kasar Janar Ali Saibu , wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar 31, ga watan Oktoban da ya gabata a Yamai, yana da shekaru 71.

An binne shi ne a mahaifarsa, Dingazy Banda da ke cikin jahar Tilabery.

Kafin jana'izar an yi addu'o'i a fadar shugaban kasa, kuma cikin wadanda suka halarta akwai

shugaban kasar na yanzu, Alhaji Isufu Mahamadu, da tsoffin shugabannin kasar ta Nijar, Malam Muhammane Ousmane, da Malam Mammadou Tandja, da Janar Salu Jibo, da kuma tsohon Praministan kasar Shehu Amadou.

Shi dai janar Ali Saibu shi ne ya mayar da kasar ta Nijar bisa tafarkin dimokaradiya ta hanyar shirya zabubbuka, tare da mika mulki ga farar hula a shekarar 1993.