Kalubalen da ke cikin batun baiwa Girka bashi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Merkel da Sarkozy

Shugabannin kasashen Faransa da Jamus sun shaidawa Girka cewa ba za ta samu karin kudi daga kasashen da ke amfani da kudin Euro ba, sai ta nuna cewa da gaske take wajen ci gaba da kansancewa a cikin kungiyar kasashen.

Shugabannin na mayar da martani ne ga matakin da Girka ta dauka na gudanar da kuri'ar raba-gardama game da bashin da kasashen tarayyar Turai suka yi alkawarin ba ta.

Idan dai jama'ar Girka suka zabi ficewa daga cikin kungiyar , hakan zai sa kasar ta gaza iya biyan bashin da ake bin ta.

Kazalika hakan na nufin tattalin arzikinta zai ci gaba da tabarbarewa, kuma tabarbarewar tattalin arzikinta zai shafi kasashen da ke amfani da kudin euro.

Shugaban Faransa da shugabar gwamnatin Jamus sun yi kira ga Girka ne a wajen taron da kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya, G20 ke yi a birnin Cannes da ke Faransa.