Rashin tabbas kan gwamnatin Girka

George Papandreou Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption George Papandreou na fuskantar matsin lamba

Ana ci gaba da zaman dar-dar a fagen siyasar kasar Girka, inda rahotanni ke nuna cewa mai yiwuwa Fira Ministan George Papandreou, ya yi murabis nan da wani dan lokaci.

Mr Papandreou zai gana da shugaban kasar Karolos Papoulias da zarar an gama taron gaggawa na majalisar zartarwar kasar - duk da cewa wasu rahotanni sun ce ba za a yi ganawarba.

Ana hasashen zai nemi a kafa gwamnatin hadin kan kasa, inda tsohon jami'in babban bankin kasar Lucas Papademos zai jagoranta.

Amma gidan talabijin na kasar ya ambato Mr Papandreou yana cewa ba zai yi murabis ba.

Gwamnatin ta Girka na gab da rushewa bayan da wasu ministoci da dama suka ce ba za su goyi bayan shirin Mr Papandreou na gudanar da kuri'ar raba-gardama kan shirin ceto kasar na Tarayyar Turai.

Wakilin BBC Mark Lowen a birnin Athens, ya ce koma ya makomar taron ta kasance, an jefa Girka cikin rudanin siyasa.

Shirin zai baiwa Girka euro biliyan 130 sannan a rage mata bashinta da kashi 50 cikin dari, domin daukar matakan tsuke bakin aljihu.

A ranar Alhamis, babban jagoran 'yan adawa Antonis Samaras ya nemi a kafa gwamnatin hadin kan kasa domin kare shirin na Tarayyar Turai.

Matsalar bashin ta kasashen euro ta mamaye agedar taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da ake yi a kasar Faransa.

Karin bayani