Jama'a a Jigawa sun yi korafi game da allurar polio

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, mazauna wasu yankuna na jihar Jigawa da ke arewacin kasar sun ce ba a yi wa iyalinsu allurar riga-kafin cutar sha-inna.

Mazauna kauyen Chiroma da ke karamar hukumar Malam Madori sun ce tun bara ba a yi wa 'ya'yansu allurar riga-kafin cutar ba duk kuwa da cewa suna cikin hatsarin kamuwa da ita.

Sai dai shugaban karamar hukumar Malam Madori, Baffa Maigari, ya ce mai yiwuwa ba a yiwa yaran allurar riga-kafin shan innan ba ne saboda a lokacin da jami'an lafiya suka je yankin mutanen da ya kamata su kai iyalansu a yi musu allurar basa nan.

Najeriya dai na cikin kasashen da ke ci gaba da fama da cutar shan inna a duniya.