An kori karar da CPC ta shigar a Katsina

Kotun saurarar kararrakin zabe dake jahar Katsina, ta kori karar da tsohon Shugaban majalisar dokoki ta kasa kuma dan takarar gwamna na jam'iyyar CPC, ya shigar yana kalubalantar zaben Gwamna Ibrahim Shehu Shema na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar katsina.

Kotun a karkashin jagorancin Mai Shari'a Florence Jombo Ofoh ta ce, ba ta gamsu da hujjojin da Alhaji Aminu Bello Masari ya gabatar ba, wadanda har yake neman Kotun ta soke zaben gwamnan da aka gudanar a kwanan baya.